An kashe mutane hamsin da biyar a kasar Syria

Smoke rises from a building in the Al Hader area of Hama.

Kungiyoyin hankoron kare hakkin jama'a a kasar Syria sunce sojojin kasar sun kashe akalla mutae hamsin da biyar a hare haren da suka kai birane biyu, inda farar hula ke zanga zangar kin jinin gwamnatin Bashar l Assad.

Kungiyoyin hankoron kare hakki jama'a a kasar Syria sunce sojojin gwamnati sun kashe akalla mutane hamsin da biyar a biranen kasar guda biyu, wuraren da farar hula suka yi zanga zangar nuna rashin amincewa mulkin kama karya ta shugaba Bashar Al Assad.

Kungiyoyin sun fada cewa akalla mutane arba'in da biyu aka kashe jiya lahadi a lokacinda sojojin Syria tare da taimakon tankokin yaki suka kaddamar da harin kafin ketowar alfijir akan birnin Deir El Zour dake gabashin kasar. Haka kuma sunce an kai hari garin Houleh inda aka kashe akalla mutane goma sha uku.

Shugaba Assad ya kare matakin murkushe masu zanga zangar, yana mai fadin cewa alhaki ne daya rataya a wuyansa na tinkarar wadanda ya kira bijirarru, wadanda suke tare hanyoyi da razana mutane. Shugaban yayi wannan furucin ne a lokacinda Ministan harkokin wajen Lebanon ya kai masa ziyara jiya Lahadi. Haka kuma yace kasarsa tana kan turba canji.

Kasashen duniya na ci gaba da matsawa shugaban lamba daya kawo karshen mumunar murkushe masu zanga zanga da yake yi. Kasar Saudi Arabiya ta janye jakadanta daga kasar, ta gabatar da sanarwar tana kira ga shugabanin Syria da su kawo karshen zubar da jini haka nan, kafin lokaci ya kure.

Kungiyar kasashen Larabawa wadda bata ce komai ba, tun lokacinda aka fara wannan tunzuri a watan Maris, itama ta gabatar da sanarwa tana kira ga shugaba Assad daya kawo karshen tarzomar nan da nan. A ranar asabar baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon ya gabatar da sanarwar makamancin ta kungiyar kasashen Larabawa ga shugaba Assad ta wayan tarho.