An Kashe Mayakan Al Shabab 30 a Somaliya

Wasu daga cikin maaykan Al Shabab masu ta da kayar baya a Somaliya da makwabtanta

Wani hari da ake zaton dakarun Amurka ne suka kai, ya yi sanadin mutuwar wasu mayakan Al Shabab su 30 a kudancin Somaliya.

Wani hari da aka kai da jirgi mara matuki ya halaka wasu mayakan Al Shabab da ake alakantawa da kungiyar Al Qaeda su 30, cikin har da manyan shugabannin kungiyar.

Dakarun Amurka ba su ce komai ba yayin da rahotannin ke cewa su suka kai harin da yammacin jiya Laraba a kusa da garin Bardere da ke yankin Gedo.

Daga cikin shugabannin kungiyar Al Shabab da aka kashe a harin akwai Jama Dere da Ismael Jabhad, in ji kakakin ma’aikatar cikin gida kasar Kenya, Mwanda Njoka.

Wani dan jarida ya gayawa Muryar Amurka cewa mataimakin kwamandan kungiyar Al Shabab a yankin Jubba da Jabhad, tsohon babban soja ne.

Garin na Bardere, mai tazarar kilomita 400 daga kudu maso yammacin Mogadishu, ya kasance wata tunga ta ‘yan kungiyar Al Shabab, inda dakarun hadin gwiwa na Habasha da Somali ke shirin kai wani farmaki domin kwato garin.