Jami’an Amurka dake bada shawarwari akan harkokin tsaro ta soki kasar Sudan ta Kudu da babban murka saboda bukukuwan samun ‘yancin kai da take yi a halin yanzu, tana mai cewa Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa kuma shugaban ‘yan tawaye Riek Machar sune musabbabin yakin da ya dai-daita kasar kuma ake cigaba da yi a kasar.
Susan Rice, tsohuwar jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta fada a wata sanarwa da ta fitar yau Alhamis cewa duk da farin cikin da Sudan ta Kudu take yi na samun ‘yancin kai a shekara ta 2011, lamarin wannan kasa na sosa mata rai matuka.
Ta ce a watanni 19 da suka gabata, gwamnatin Sudan ta Kudu ta kauracewa ayyukan da suka rataya a wuyanta, inda ta gagara tsaron rayuka da kadarorin ‘ya’yanta, kuma tayi fatali da ingancinta, yayinda tashe-tashen hankula suke cigaba tare da rigingimun siyasa.