An Kashe Gwamnan Jeka-Na-Yikan Birnin Mogadishu Na 'Yan Kungiyar Al-Shabab

Harin da aka kai ta sama ya auna wasu motoci guda biyu da 'yan bindigar ke ciki akan hanyar Buula-Banin, A yankin Shabelle

Wani jami’in ma’aikatar tsaron Amurka ya tabbatarwa Muryar Amurka cewa an kashe gwamnan jeka-na-yika na birnin Mogadishu da ‘yan kungiyar al-Shabab suka nada a wani hari ta sama da Amurka ta kai,.

An san Ali Mohammed Hussein, wanda kuma ake kira Ali Jabal, da tilastawa ‘yan kasuwa su ba mayakan al-Shabab kudi.

A wata sanarwa akan harin daga dakarun Amurka dake aiki a Afrika, ta ce an kai harin ne da yammacin ranar Asabar, ta kuma kara da cewa babu farar hula ko daya da ya rasa ransa.

Haka kuma sanarwar ta ce harin ta sama da aka kai, an yi shi ne da hadin gwiwar dakarun kawancen dake yankin “a matsayin maida murtani akan matakan da kungiyar al-Shabab ta dauka, ciki harda hare-haren da kungiyar ta kai kwanan akan dakarun Somaliya.