Gwamnatin kasar Kamaru ta gano gawarwaki goma sha daya na dakarun tsaronta cikin talatin da hudun da suka nitse cikin teku a kan hanyarsu ta zuwa Tsibrin Bakassi.
Shi Tsibirin Bakassin dake kan iyakar kasar da Tarayyar Najeriya yana da arzikin man fetur.
Hatsarin da ya nitse da sojojin na Kamaru ya faru ne tun ranar 16 ga wannan watan Yulin.
Ministan tsaron kasar Victor Asumo shi ya jagorancin bikin karrama gawarwakin sojojin da dakarun tsaro guda uku wadanda suka tsira da rayukansu. Ministan yace Shugaban kasar Paul Biya ya umurceshi ya makala masu lambobin yabo tare da cewa sun zama jarumai wajen kare kasarsu.
To saidai har yanzu akwai gawarwaki 22 da ba'a ganosu ba lamarin da ya sa mahukumtar kasar suka rungumi kaddara cewa su ma sun mutu cikin hadarin.
Musa Useini dan kungiyar kwato hakkin bil Adama yace duk wani mutum da ya samu kansa a wani al'amari yana da hakkin a gano abun da ya faru dashi. A bincika a san dalilin aukuwar lamarin. Ya zargi gwamnatin kasar da yin sakaci wajen kwato wa mutane hakkinsu.
Inji Musa Useini samun gawarwaki 11 ya nuna za'a iya samun sauran idan aka ci gaba da bincike.
Alhaji Ribadu Sharubutu dan siyasa kuma daya daga cikin kwamitin gano gawarwakin da gwamnati ta kafa yace mutane su sani hatsari ne ya faru. Cikin wadanda suka rasu akwai musulmi wanda aka kara masa girma bayan rasuwarsa. Ya bada gaskiya za'a gano sauran gawarwakin.
Ga rahoton Awal Garba da karin bayani.
Facebook Forum