‘Yan sanda a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo sun kama fiye da masu zanga zanga 100 a birane daban-daban na kasar, bayan da suka yi kiran a gudanar da zaben shugaban kasa a karshen shekarar nan.
An yi zanga zangar ce a Kinshasa, babban birnin kasar, da birnin Goma da ke gabashi, da wasu biranen kasar da dama.
Wadanda suka shaida boren a birnin Goma, sun ce ‘yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga zangar, yayinda a Kinshasa kungiyoyin manema labarai suka ce an tsare ‘yan jarida da dama na dan wani lokaci.
A jiya Litinin, ofishin kare hakkin bil adama na hadin gwuiwa da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya a Congo, ya yi Allah wadai da tsare masu zangar zangar da aka yi, yana mai cewa, “kama mutane ba bisa ka’ida ba ya yi hannun riga da yunkurin neman bayanai da kuma ‘yancin yin taro,” wadanda duk kundin tsarin mulkin Congo ya ba da damar a yi.
A watan Disamban da ya gabata, wa’adin mulkin da doka ta tanadawa Shugaba Joseph Kabila ya cika, wanda shi ne na biyu na kuma karshe, lamarin da ya haifar da tarzomar siyasa a kasar.
Facebook Forum