Majalisar dokoki a Jamhuriyar Nijar ta sake aiwatar da kwaskwarima ga wasu dokokin zabe a karo na biyu.
An yi sauye-sauyen ne bayan da kotun tsarin mulki ta yi watsi da gyaran fuskar da aka wa dokokin a karon farko lura da yadda matakin ya sabawa kundin tsarin mulki.
A lokacin wannan zama, da majalisar ta gudanar domin gyaran dokokin, ‘yan hamayya sun sake kauracewa zauren majalisar inda suka yi ikirarin cewa yunkurin yin magudi ne a zabe mai zuwa.
Bangarorin da sauye-sauyen suka shafa sun hada da tsayar da ranakun zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da kuma kayyada ajiye takardun ‘yan takara da kuma wa’adin shigar da kara a gaban kotun tsarin mulki.
Sannan sai ka’idodin kafa hukumar zabe mai zaman kanta.
Dan majalisa Lamido Mumuni Haruna, ya fadawa Muryar Amurka cewa ba su da tababa, wannan aiki yana da sahihanci.
“Yanzu ina ganin wannan kundi ya dace.” In ji Dan majalisa Haruna.
Sai dai tuni masu sharhi irinsu Abdurraham Al Kasim suka fara sukar wannan mataki da aka dauka.
“Duka dai magana da ake yi ta maganar shirya zabubbuka ne, musamman wacce ta fi kusa da na maye gurbin dan majalisa na jihar Maradi, tunda farko kotun tsarin mulki ta yi kira kada a wuce kwana 60 ba tare da an yi zabe ba.” A cewar Al Kasim.
Ya kara da cawa, “Da farko shugaban kasar ya yi kiran a yi hakan, amma ya koma ya dauki wani mataki wanda ya karya matakin kotun tsarin mulki wanda ba shi da hurumin ya yi hakan.”
Bangaren ‘yan hamayya a majalisar ya nuna rashin gamsuwarsa da wannan mataki.
“Mu mun ja hankalinsu, mun ce akwai matsaloli da yawa, an yi kuskure, abinda duk ake yi ana magudi ne don a samu a kare mutum guda." In ji Kakakin 'yan adawa Isuhu Ishaka.
Saurari rahoton Sule Mumuni Barma domin jin karin bayani:
Facebook Forum