WASHINGTON, D. C - Wasu da dama kuma sun jikkata, a cewar sanarwar wacce aka karanta a kafar talbijin inda bayanai suka nuna cewa wannan adadi na wucin gadi ne.
'Yan ta da kayar bayan sun kai hari kan wani jirgin ruwa dauke da fararen hula da ke kan filayen da ambaliyar ruwa ta raba tsakanin garuruwan Gao da Mopti a lokacin damina.
Jirgin ruwan yana tafiya ne daga Gao lokacin da aka kai harin.
Maharan sun kuma kai hari a wani sansanin soji da ke yankin Bourem Circle da ke arewa maso gabashin Mali.
Kimanin maharan 50 ne aka kashe a matsayin mayar da martani, an kuma ayyana zaman makoki na kwanaki uku, in ji gwamnatin wucin gadi.
Kasar Mali dai na daya daga cikin kasashen yammacin Afirka da ke fama da tashe-tashen hankula masu alaka da kungiyar Al Qaeda da IS da suka samu tushen zama a Arewacin kasar tun shekarar 2012.
Mayakan sun samu galaba, sun kuma bazu a yankin Sahel da kuma kasashen yammacin Afirka da ke gabar teku, duk da dumbin kudade da kasashen duniya ke bayarwa na tallafa wa sojojin kasar.
Dubban mutane ne aka kashe tare da raba sama da miliyan shida da muhallansu a fadin yankin Sahel da ke kudu da hamadar Sahara.
Takaici game da karuwar rashin tsaro ya haifar da juyin mulkin sojoji a Mali da Burkina Faso tun daga shekarar 2020 - hudu daga cikin juyin mulki takwas da aka yi a Yamma da Tsakiyar Afirka cikin shekaru uku da suka gabata.
-Reuters