An Kashe Dan Shugaban IS Abu Bakr al-Bagdadi a Wani Hari

Shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Bagdadi

Dan shugaban kungiyar IS Abu Bakir al-Bagdadi ya mutu a wani harin kunar bakin wake da ya kai a birnin Homs a yammacin Syria, bisa ga cewar kafar labaran IS al-Nashir.

Kafar sadarwar IS al-Nashir ta buga hoton matashin da aka bayyana a matsayin Hudhayfah al-Badri, dan al-Baghdadi, ya rasa ransa ne yayin wani hari da ya kai kan dakarun kasar Rasha da na gwamnatin Syria da kungiyar IS ke kira Nusayriyyah, da aka girke a Homs.

Muryar Amurka bata tabbatar da mutuwar tasa ba.

Al-Baghdadi wanda dan asalin kasar Iraq ne , wanda ainihin sunansa shine Ibrahim Awad al-Badri, ya ayyana kafa daukar Musulunci ne a birnin Mosul a watan Yuni shekara ta 2014, ya kuma mayar da kansa Kalifa. shugaban kungiyar ta IS, ya kasance mutum da aka fi nema ruwa a jallo a duniya, wanda kuma aka yi alkawarin bada tukuicin dala miliyan ishirin ga duk wanda ya bada bayanan da zasu kai ga kamashi.

Kawo yanzu babu tabbacin inda Al-Baghdadi yake, yayin da wadansu rahotanni marasa tushe suka sha cewa an kashe shi ko kuma an ji mashi rauni.