Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Thailand: Matasan Da Suka Kwashe Kwana 10 A Kogo An Samesu Da Rai


Wasu jami'an Amurka na musamman da suka shiga aikin ceto 'yan wasan kwallon da suka makale a wani kogo a kasar Thailand
Wasu jami'an Amurka na musamman da suka shiga aikin ceto 'yan wasan kwallon da suka makale a wani kogo a kasar Thailand

Matasa 12 da mai horas dasu a wasan kwallon kafa da suka makale a wani kogo a kasar Thailand an samesu da rai

An samu matasa goma sha biyu ‘yan wasan kwallon kafa na kasar Thailand da mai horon su da rai cikin wani kogo kwanaki goma bayan sun bace.

Jiya Litinin gwamnan lardin Narongsk Oscthanakcon ya fadawa yan jarida cewa an samu matasan kuma dukkansu suna da rai. Yace za’a kawo likita ko kuma liktoci da zasu kula da su har sai sun murmure. Yace bai tabbatar ko zasu iya cin abinci nan take ba domin sun dan kwana biyu basu ci komai ba.

Su wadannan matasa yan shekara tsakanin sha daya zuwa sha shidda da mai horon su, mayakan ruwa na musamman ne suka same su makale cikin kogo.

Jiya Litinin mayakan ruwan masu aikin ceto suka ceci matasan a gefen kogon dake kan tudu..

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG