Ana sa ran ganin karin masu zanga zangar adawa da sabuwar dokar sashen shari’ar kasar Poland a yau Laraba, yayin da dubban masu macin ke fadin cewa wannan mataki ne da gwamnatin masu ra’ayin neman sauyi take dauka na mamaye kotunan kasar.
An ga dubban masu zanga zanga dauke da tutocin Poland da na Tarayyar Turai kuma suna ihu suna cewa kada a mamaye kotuna a cikin birnin Warsaw da wasu biranen kasar a jiya Talata.
A karkashin sabuwar dokar da ta rage shekarun yin ritaya ga alkalan manyan kotuna, sama da kashi uku cikin hudu na alakalan kotun koli ne za a tilastawa su yi ritaya a yau Laraba.
Wanda ya kafa kungiyar kwadago ta Solidarity, wanda kuma ya taba cin lambar yabo ta Nobel Prize, Lech Walesa, (LAKE VAWENSA) yace yana cikin wadanda zasu yi maci a yau Laraba, yana mai cewa a shirye yake ya jagoranci shirin tsige Firai ministan kasar Jaroslaw Kaczynski kuma shugaban jami’iyar Law and Justice mai mulki da karfin tuwo, wanda yace shine sanadin matsaloli da kasar ke huskanta.
Sai dai Walesa bai yi wani karin bayani game da abin da yake nufi da tsigeshi da karfin tuwon ba.
Gwamnati tace wajibi ne a kawo suayi a sashen shari’ar kasar, tana mai cewa galibin dokokin sashen an yi su ne tun zaman tsarin mulkin kwamisanci.
Facebook Forum