A watan da ya gabata Ibrahim Alfa da Halima Djimrao da shugaban sashen hausa Leo Keyen sun samu lambar yabo na zinari a bisa kwarewa kan aiki.
WASHINGTON, DC —
Hukumar Gidan Rediyon muryar Amurka ta karrama wasu mutane da lambar yabo mafi girma na gidan Rediyon.
Ibrahim Alfa Ahmed, ya kasance daya daga cikin wadanda suka sami wanna lambar ta yabo sakamakon hazaka da sadaukar da yaruwa wajen neman labarai.
Hukumar gidan Rediyon kara da cewa irin yadda Ibrahim Alfa ke bin kadin labarai domin fayyace gaskiya abun a jinjinamasa ne.
Da yake jawabi akan wannan karamci da akayi masa ya godewa hukumar muryar Amurka da ma'aikatan sasahen Hausa wadanda yace sun taimaka gaya ga wannan nasara daya samu.
A watan da ya gabata Ibrahim Alfa da Halima Djimrao da shugaban sashen hausa Leo Keyen sun samu lambar yabo na zinari a bisa kwarewa kan aiki.