Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Republican Masu Takarar Shugaban Kasa Sun Yi Muhawarar Karshe


'Yan Republican su tara da suka yi muhawara jiya a birnin Las Vegas dake jihar Nevada
'Yan Republican su tara da suka yi muhawara jiya a birnin Las Vegas dake jihar Nevada

‘Yan takarar neman shugabancin Amurka a karkashin jam’iyar Republican su tara, sun karkata hankulansu akan batun tsaro da ayyukan ta’addanci, yayin da suke yin muhawararsu ta biyar a daren jiya Talata.

Muhawarar wacce aka yi a birnin Las Vegas da ke jihar Nevada, ta gudana ne, kasa da watanni biyu kafin a tunkari muhimmin taron da jam’iyyar za ta yi a Iowa, domin share fagen zaben fidda gwanin da za ta tsayar a matsayin dan takararta.

An fara muhawarar ce da Donald Trump, wanda ke sahun gaba a karbuwa, kan batun furucin da ya yi na cewa a haramtawa Musulmi shiga Amurka na dan wani lokaci.

Trump, wanda hamshakin dan kasuwa ne a fannin sayar da gidaje, ya kare furucinsa, inda ya ce, shi ba magana ya ke yi akan addini ba, illa batun da ya shafi tsaro.

Ya kuma kara da cewa, ya fahimci cewa furucin na sa ya janyo babbar muhawara, wacce tun-tuni ya kamata a fito fili a yi ta kan masu tsatsauran ra’ayin Islama ganin cewa akwai Amurkawa da suka yi na’am da bukatar.

Sai dai tsohon gwamnan jihar Florida, Jeb Bush, wanda ba ya dasawa da Trump, ya caccaki matsayar ta Trump, wacce ya kwatanta a matsayin abin da ba zai yiwu ba, domin hakan zai iya kawo cikas ga yakin da ake yi da IS, yayin da Sanata Ted Cruz na Texas dake samun karbuwa a ‘yan kwanakin nan, shima ya ce ba ya so a maida wani addini saniyar ware, sai dai a yaki duk wata tsautsarar akida da ke neman halaka mutane.

XS
SM
MD
LG