Bisa duka alamu kungiyar kwadagon jihar Neja da gwamnatin jihar sun shiga wani takunsaka akan batun fansho.
Kungiyar kwadagon ta ki ta halarci wani taro da gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya kira akan batun tsarin fanshon da gwamnati ke anfani dashi. Ya kira taron ne domin tattaunawa akan sabon tsarin.
Kakakin gwamnan jihar Jibril Baba Ndagi yace duk da rashin halartar kungiyar kwadagon sun gudanar da taron. Yace sun yi wajen awa uku suna tattaunawa akan hanyoyin cin nasara.
Amma su 'yan kungiyar kwadagon sun ce basu samu takardar gayyata ba kamar yadda Idris Ndako shugaban kungiyar ya fada. Yace idan basu da takardar gayyata 'yansandan dake bakin gidan gwamnati ba zasu barsu su shiga ba.
Saidai duk da yake shugaban majalisar dokokin jihar ya halarci zaman amma shugaban kwamitin dake kula da harkokin ma'aikata na majalisar dokokin Malik Madaki Boso bai amsa goron gayyatar gwamnan ba. Yace tunda maganar tana gabansu kamata ya yi a dakata sai sun gama aikinsu kafin a yi wani taron.
Ga karin bayani.