Wani madugun ‘yan adawa a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, ya ayyana cewa sun balle da wani bangaren arewacin kasar, bayan da suka yi watsi da zaben raba-gardama da aka yi da nufin daidaita kasar.
Mai Magana da yawun Noureddin Adam, wanda ke jagorantar mayakan Seleka, ya ce sun sakawa sabon yankin suna “Jamhuriyar Logone” wanda aka kafa a ranar 14 ga watan Disamba a garin Kaga-Bandoro.
Hedkwatar wannan bangaren mayakan na Seleka na wannan gari ne Kaga-Bandoro, wanda ke da tazarar kilomita 250 daga arewacin Bongui, babban birnin Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya.
Kakakin kungiyar mai suna, Mauloud Moussa, ya kara da cewa ballewar da suka yi, mataki ne na farko kafin su nemi ‘yan cin gashin kansu.
Duk wannan dai na faruwa ne, yayin da ‘yan kasar su ke dakon sakamakon zaben raba-gardama da aka yi a ranar Lahadi kan kundin tsarin mulkin kasar.
Sai dai an kara lokacin zaben har zuwa Litinin a wasu yankunan kasar, saboda hatsaniyar da aka samu wacce hukumar ba da agajin gaggawa ta Red Cross ta ce an kashe akalla mutane 20.