An Kara Yawan Sojoji a Yankin Arewa

Jami'an Tsaro

Kasashen dake makwabtaka da Najeriya sunyi alkawarin bada bataliya guda-guda na hadin gwiwa domin tsare yankin arewa maso gabas.
An kara Sojoji kusan dubu biyar a yakin arewa maso gabashin Najeriya domin tunkaran ‘yan boko haram,wa’anda suka addabi jama’ar yankin.

Shugaban hukumar kyautata rayuwar jama’a, Mr. Mike Omeri ne ya bayana haka a hiran da sukayi da wakilin mu Aliyu Mustapha ta wayan tarho.

Inda yace shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi alkawarin cewa zaiyi duk abunda zai iya da hadin gwiwa da kasashen Afirka dama na duniya baki daya da kuma hadin kan ‘yan Najeriya domin shawo kan wannan matsalar da ta addabi Najeriya.

Yace sojojin Najeriya da sojojin waje da suka kawowa Najeriya dauki na ci gaba da yin aiki tare domin ganin cewa an samu tsirada ‘yan makarantar da aka sace a garin Chibok.

Mr. Omari ya kara da cewar kasashen dake makwabtaka da Najeriya sunyi alkawarin bada bataliya guda-guda na hadin gwiwa domin tsare yankin arewa maso gabas.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kara Sojoji a Yankin Gabashin Arewa - 4'26"