Shugaban Amurka Donald Trump ya kara tsawon wa’adin jinkirta harajinsa akan karafuna da dalma da ake shigowa da su daga kasashen Turai, irinsu Canada, da Mexico, har zuwa akalla wata daya.
Dama yau Talata ne shirin jinkirta harajin na dan wani lokaci akan kasashen na Turai, wanda tuni ya fara aiki kan China da Japan da Rasha, zai kare.
Hukumar tarayyar Turai ta yi Allah wadai da jinkirta harajin na dan wani lokaci kawai, a wata sanarwa da ta fitar yau Talata, ta na mai cewa tarayyar Turai ta so ne a tattauna batun, kuma ba za ta hau teburin shawara ba da barazana.
Shugaba Trump ya kira shirin harajin “batun tsaron kasa” saboda yadda yawan kayayyakin wasu kasashe suka sa kayayyakin Amurka da ake kaiwa ketare yin tsada, kuma ba a bukatarsu sosai a kasuwannin duniya.