Taron na kwana ɗaya, ya tattauna kan yanayin da ake ciki a Mali bayan juyin mulkin da soji suka yi wa Shugaba Ibrahim Boubakar Keita a ranar 18 ga Agusta, lamarin da ya sa ECOWAS ta sanya wa ƙasar takunkumi.
Taron ya kuma tattauna matsalolin annobar COVID-19 da tattalin arziki da tsaro a nahiyar baki daya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a jawabin da yayi a wajen taron, ya gargadi ‘yan uwansa shugabannin kasashen Africa ta Yamma da suyi takatantsan akan yunkurin da wadansu ke yi na neman dawwama akan karagar mulki.
Buhari ya ce hakan kan kawo tashe-tashen hankula da fargaba akan zaman lafiya a yankin na Afrika ta Yamma, wanda a yanzu haka yake fama da matsaloli da dama kamar na tattalin arziki, da na tsaro da na zamantakewa.
Shugaba Buhari ya kuma yi gargadi akan barazanar sojojin da su kayi juyin mulki a kasar Mali, inda yake cewa ya goyi bayan matsayar da ECOWAS ta cimma na ba su wa’adin shekara daya su tabbatar sun mika mulki ga farar hula da zai jagoranci gwamnatin rikon kwarya da za ta shirya zabe a cikin shekara daya, idan suna so ayi musu rangwame akan takunkumin da kasashen Afrika a yanzu suka kakabawa kasar.
Wani mai sharhi akan al’ammuran yau da kullum, kuma shugaban wanzar da demokradiyya a Najeriya Professor Jibrim Ibrahim ya ce “yanzu kasashe da dama a Afrika ta Yamma shugabanninsu sun fito suna neman su yi tazarce," akan haka ya yabawa shugaba Buhari da ya fito ya gaya musu illar da ke tattare da wannan burin na su.
A wajen taron an zabi shugaban kasar Ghana Nana Akufor Addo a matsayin sabon shugaban kungiyar ta ECOWAS, inda ya karbi shugabancin daga hannu shugaban Kasar Nijar, Muhammadou Issoufou.
Saurari cikakken rahotan Umar Faruk Musa:
Your browser doesn’t support HTML5