Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Mali Boubacar Keita Ya Yi Murabus


 Shugaban Kasar Mali Boubacar Keita
Shugaban Kasar Mali Boubacar Keita

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya yi murabus da daren jiya Talata, ‘yan sa’o’I bayan da sojoji suka kama shi biyo bayan kwashe watanni ana gudanar da garumar zanga-zanga..

A jawabin da ya yi ta gidan talabijin din kasar, Keita mai shekaru 75 a duniya, ya ce baya son a zubar da jini don ya ci gaba da Mulki

Jiya Talata aka kama Keita da Firai minista Boubou Cisse a babban birnin Bamako. Wakilin sashen Faransanci na Muryar Amurka, ya ce sojoji sun dauki Keita Cisse zuwa sansanin soji dake Kati.

Kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta rufe iyakokin kasashe dake makwabtaka da Mali, bayan kama Keita da fara ministansa, haka kuma ta soke dukkan duk wasu harkoki tsakanin kasashen mambobinta 14 da kasar Mali.

Hakan ya biyo bayan bore da wasu sojojin kasar suka yi ne tun da safiyar Talata, bayan sojojin sun yi harbe-barbe a iska a wani sansani dake Kati, kusa da babban birnin kasar Bamako.

Rahotannin sun ce sojojin da suka yi boren suna kuma tsare da wasu manyan jami’an gwamnati da wasu manyan sojoji.

Wannan lamari ya biyo bayan makwanni da aka shafe ne ana takaddamar siyasa a kasar.

Wani sojan kasar Mali
Wani sojan kasar Mali

Tun da farko a ranar Talata din, tsohon shugaban kasa a Najeriya, Goodluck Jonathan ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar domin ya sanar da shi halin da ake ciki a game da rikicin siyasar kasar ta Mali, bayan ya ziyarci kasar a makon jiya a ci gaba da kokarin sasanta bangarorin dake takaddamar.

Idan ba a manta ba, an ga Tsohon Shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, a kasar Mali daga ranar Litinin zuwa Alhamis a cikin makon da ya gabata, inda ya gana da masu ruwa da tsaki hade da shuwagabannin siyasa da na addini.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG