Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batutuwan Da Shugabannin ECOWAS Za Su Tattauna Akai


Wasu shugabannin ECOWAS
Wasu shugabannin ECOWAS

Shugabanin kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka ta ECOWAS za su hadu a yau a birnin Yamai na jamhuriyar Nijer don tantaunawa akan wasu mahimman batutuwan da suka shafi kasashen yankin.

Batun takardar kudadin bai daya wato ECO da ya kamata a soma amfani da ita a wannan shekara ta 2020 na daga cikin mahimman batutuwan da shuwagabanin kasashen ECOWAS ke tantaunawa akansu.

Za su duba hanyoyin warware daurin kan dake tattare da wannan shiri bayan da kasashen Afrika ta yamma renon Faransa suka ayyana yunkurin soma amfani da kudin na ECO duk kuwa da cewa ainihi CEDEAO ke da wannan kudiri inji shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou mai masaukin baki.

ECOWAS
ECOWAS

Taron wanda ke gudana a dai dai lokacin da shugaba Issouhou Mahamadou ke kammala wa’adin shugabancin kungiyar ta ECOWAS zai saurari shawarwari daga bakin shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a game da matakan yaki da cutar coronavirus a matsayinsa na gwarzon yaki da wannan anoba a yankin Afrika ta yamma.

Kana za su tattauna kan yanayin da ake ciki a kasar Mali bayan juyin mulkin da ya kawarda Ibrahim Boubacar Keita daga karagar mulki.

Daga bison wannan zama zai dubi sha’anin tsaro a wannan yanki wanda ke ci gaba da tabarbarewa.

Saurari cikakken rahoton Sule Barma cikin a:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:59 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG