Kawo yanzu hukumar bada agajin gaugawa ta babban birnin tarayya (FEMA) ta ce ta kammala aikin ceto wadanda rushewar wani bene hawa hudu ya rutsa dasu a birnin Abuja.
WASHINGTON D.C. —
Darakta Janar na hukumar Alhaji Abbas Idriss ya shaidawa Muryar Amurka cewa kimanin mutane takwas ne abin ya rutsa dasu, amma mutane biyu sun rigamu gidan gaskiya.
Alhaji Abbas Idriss ya ‘kara da cewa yawan rushewar gine-gine a babban birnin Abuja na daminsu, al'amarin kenan ma da yasa suke shirye-shiryen daukar mataki.
Shi dai wannan Gini an fara gininsa ne tun kimanin Shekarau 20, amma akai watsi da aikin har sai kwanan nan aka ci gaba da aikin ba tare da tantance nagartarsa ba.
Daga nan darakta janar na hukumar bada agajin gaggawan ya nemi masu ruwa da tsaki a harkar gine-gine da su ‘kara maida hankali wajen bin sharudda da ka'idojin gine-gine don kiyaye ci gaba da samun hakan.