Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Gina Tashar Motoci Ta Zamani A Obolo Afor Da Ke Jihar Enugu


Bikin sanya hannu domin gina tashar motoci ta zamani a Obolo Afor dake jihar Enugu
Bikin sanya hannu domin gina tashar motoci ta zamani a Obolo Afor dake jihar Enugu

An yi bikin sanya hanu kan amincewa da yarjejeniyar gina tashar manyan motoci ta farko ta zamani a Nigeria tsakanin hukumar kula da yarjeniyoyin hadin gwuiwa da gwamnatin Nijeriya “CONCESSION REGULATORY COMMISSION” da hukumar hada-hadar kasuwanci ta jiragen ruwa.

Tashar ta farko za'a ginata ne a garin Obollo-Afor dake jihar Enugu, inda tuni aka samu katafaren fili mai tsawon kadada 16, kuma zata dauki dukkan manyan motoci da kan tsaya a garuruwan dake kan manyan hanyoyin da hakan kan haddasa cunkoso da ma hatsari,.

Wakili a hukumar kula da wadannan tashoshi Injiniya K.C. Izuwah yace ya kamata gwamnatin Nigeria ta kafa duka a zata tilasta direbobi su rika tsayawa don hutawa; don an gano yawancin direbobin kan yi barcin sa’a 4 ne kacal cikin sa’o’I 24 inji Injiniya Chidi K.C. Izuwah.

Ya ci gaba da cewa akwai bukatar samar da tashoshin madakatar manyan motocin domin direbobi su samu su huta a kuma kaucewa hadarin da kan faru a kan hanyoyi sanadiyar ajiye manyan motocin a gefen tituna

Izuwah ya ce tashoshin na zamani za su zama da masaukan baki,gidajen abinci, bankuna, asibitoci, kotuna, wuraren ibada, makanikai har ma da wajen shakatawa da wanke motoci.

Shugaban hukumar zirga-zirgar harkar kasuwanci ta jiragen ruwa Hassan Bello, ya ce za a fara aikin nan take kuma za a kafa irin tashoshin a duk garuruwan da manyan motoci ke tsayawa, baya ga rage hatsaari, zai kuma bunkasa tattalin arzikin al’ummar yankunan.

Kungiyar direbobi da ake kira NURTW a takaice data masu manyan motocin sufuri wacce ake kira NARTO a takaice, sun amince da shiga wannan tsari don inganta rayuwar direbobin da kula da lafiyar motocin.

A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG