An Kama Wani Mutum Da Harsasai 900 A Kan Iyakar Najeriya

Sfeto-Janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idriss

Rundunar 'yan sanda jahar Sokoto tayi nasarar kama wani mutum da ya yi yinkurin tsallakowa daga kan iyaka Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya dauke da harsasai guda dari tara.

Yanzu haka a garin Araba da ke cikin karamar hukumar mulkin Illela da ke cikin jahar Sokoto a Najeriya, wanda kilomita biyu ne daga garin Kaura na garin Birnin Konni da ke cikin jahar Tawa a Jamhuriyar Nijar, ana zaman dardar.

Hukumar ‘yan sanda ta karamar hukumar ta Illela sun kama wani mutum dauke da harsasai guda dari tara yayin da yake kokarin tsallaka kan iyakar Birnin konni zuwa iyakar Ilella.

Sarkin Arewa Araba Alhaji Abubakar Isuhu, ya fada wa wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Harouna Mamane Bako, cewa ‘yan sandan sun yi nasarar kama wani mutum da ke kan mashin tare da dan kabu-kabun da yake tuka shi.

Sannan basaraken ya kara da cewa mutumin dake dauke da harsashen guda dari tara, yayi kokarin bawa jami’an ‘yan sandan cin hancin makudan kudade domin su barshi ya wuce. Yanzu haka hukumomin Birnin Nkonni da Bagaruwa sun baza jami’an tsaro a kan iyakar Jamhuriyar Nijar da Jahar Sokoto ta Najeriya domin dakile dukkan wata aniya ta miyagun mutane.

Ga Harouna Mamane Bako da cikakken rahoton

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan sanda Sun Kama Wani Mutum Da Harsasai 900 A Kan Iyaka Najeriya