Yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, sarakunan gargajiya da masu fada a ji na kara kaimi wajen fadakar da al’umma, kan muhimmancin gudanar da zabe ba tare da tashin hankali ba.
A wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence ta shirya a jihar Nasarawa, sarakunan gargajiya, sun jaddada cewa jama’a su zabi shugabannin da suka dace, amma su kauracewa duk wani sanadin da zai kawo tashin hankali da rasa rayuka.
Mai martaba sarkin Keffi a jihar ta Nasarawa, Shehu Chindo Yamusa, ya yi kira ga al’umma da su gudanar da zabe cikin tsanaki.
Wakiliyar sashen Hausa Zainab Babaji ta aiko da wannan rahoton.
Facebook Forum