Ministan muhalli na Najeriya, Alhaji Ibrahim Usman Jibrin, ya ajiye aikinsa bayan da aka zabe shi a matsayin sabon Sarkin Nasarawa.
Alhaji Jibrin ya mika takardar murabus dinsa ga shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da ake taron mako-mako na ministocin gwamnatin Najeriya a yau Laraba, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Buhari ya nada Alhaji Jibrin a matsayin ministan muhalli a shekarar 2015.
A farkon watan nan aka zabi Alhaji Jibrin a matsayin wanda zai maye gurbin Sarkin Nasarawa, Alhaji Hassan Ahmed Abubakar II, wanda ya rasu a farkon watan Nuwamba.
Sarki Abubakar ya rasu yana mai shekaru 83 bayan da ya yi fama da rashin lafiya.