Kimanin makonni uku da suka gabata ne ‘yan sanda suka kama wani mai suna Malam Aminu Ali Shana shugaban Jam’iyyar APC a mazabar Yautan Arewa a karamar hukumar Gabasawa ta nan Jihar Kano bisa samun sa da katunan zabe kunshe a cikin buhu har sama da dari uku.
Ya zuwa yanzu dai babu wasu cikakkun bayanai daga ‘yan sanda dangane da wannan batu koda yake tun lokacin da lamarin ya faru sun ce suna bincike.
Sai dai a nasu bangaren kungiyoyin gwagwarmayar shugabanci na gari sun sha alwashin ci gaba da bibiyar maganar domin tabbatar da cewa, dokokin kasa da na hukumar zaben Najeriya sun yi aiki kamar yadda ya kamata, kuma an hukunta wannan mutum bisa ka’ida.
Ku Duba Wannan Ma Sai Mun Tabbatar Mutum Dan Kasa Ne Kafin A Yi Ma Sa Regista-INECComrade Kabiru Sa’idu Dakata na gamayyar kungiyoyin fararen hula a Kano masu rajin demokaradiyya da shugabanci nagari ya ce akwai bukatar ‘yan sanda su fito suyi bayani a fili domin jama’a su san halin da ake ciki.
Ya ce “abinda ya kamata shi ne ‘yan sanda su bayyana wa al’umma halin da ake ciki kuma su sanar da matakan da aka dauka har zuwa kotu, domin al’umma su gamsu cewa, hukumomi sun yi adalci, ta yadda sauran ‘yan siyasa zasu koyi darasi”
Hon Aminu Muhammad Adam dake takarar majalisar wakilan Najeriya daga mazabar Gwale a inuwar Jam’iyyar PRP ya ce, “muna kira ga hukumar ‘yan sanda ta gurfanar da wannan mutum a gaban kotu domin wanzar da adalci, kuma muna kira ga hukumar zabe ta tabbatar da daukar matakan da suka kamata, da nufin gudanar da sahihin zabe a shekara ta 2023 dake tafe”.
A bayaninsa, sakataren Jam’iyyar APC ta Jihar Kano Hon. Ibrahim Zakari Sarina ya ce, ‘yan sanda sun mika batun ga kotu, amma dai ba’a kai ga fara shari’a ba tukuna, kuma ya ce sun shirya tsaf domin kare ‘dan jam’iyyar su a duk lokacin da aka fara sauraron shari’ar.
Ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoton, ofishin Kano na hukumar zaben Najeriya INEC bai ce komai ba dangane da wannan lamari.
Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5