Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Bukaci 'Yan Sanda Su Rike Amana Don Tabbatar Da Kyakkyawan Sakamako A Zaben 2023


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci rundunar ‘yan sandan Najeriya da ta kammala shirye-shiryen gudanar da ayyukan da za su tabbatar da kyakkyawan sakamako a zaben 2023

Shugaba Buhari ya kuma bukaci da su ci gaba da kasancewa da rikon amana, da biyayya ga tsarin dimokuradiyya, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar ta ce.

Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a wajen bude taron kwanaki uku na manyan jami’an ‘yan sanda. Ya kuma umurci ‘yan sanda da su sake duba matsalolin tsaro da ke faruwa a cikin gida a halin yanzu domin hakan na iya yin tasiri ga zaben cikin lumana da nasara.

“Kamar yadda na sha lura, zabuka na cikin gida ne, kuma sai a lokacin da kuri’un da aka kirga da gaske ne za a iya nuna imanin ‘yan kasa a tsarin dimokaradiyya tare da tabbatar da halaccin gwamnati.

“Wannan shi ne abin da a wannan rana da kuma wannan lokaci, na umarci rundunar ‘yan sandan Najeriya da ta yi wa al’ummar kasa a lokacin babban zaben 2023.

Shugaba Buhari ya ba da misali da yadda ‘yan sanda suka gudanar da zabukan fitar da gwanin da aka yi a wasu jihohin baya bayan nan a wasu jihohi.

Shugaba Buhari ya kuma yi amfani da wannan dama wajen sake jaddada aniyar sa ta kafa tsarin zabe na gaskiya da adalci wanda ta hanyar sa ‘yan Najeriya ke zaben shugabannin da suke so.

Shugaba Buhari ya kuma lissafta amincewa da sabon tsarin albashi da walwala wanda ya dace da biyan albashin jami’an ‘yan sanda bisa ka’idojin aikinsu.

XS
SM
MD
LG