An Kama Mutane Dubu a Neja-Delta

[FILE PHOTO]

Ya zuwa yanzu, barnar 'yan tsagera a yankin Neja-Delta bai kare ba, duk da cewa sabuwar gwamnatin Najeriya ta dauki alwashin durkusar da duk wani mai tayar da zaune tsaye.

A baya-bayannan ne dai, shugaban rundunar tsaro ta Najeriya Air Mashal Alex Badeh ya ziyarci babbar shedkwatar rundunar gamayyar jami’an tsaron yankin Neja-Delta wato JTF dake birnin Yanagowan Jihar Bayelsa, inda a cikin jawabinsa ya bayyana cewa rundunar sojan Najeriya ta samu bayanan sirri kan cewa wasu matasa a yankin Neja-Delta na shirin sake daukar makamai, musamman domin kai hare-hare a harabobin da ake ayyukan hakar danyen mai, inda kuma ya tabbatar da cewa rundunar tsaron ba zata saka bada dama ba, na dawo da tsageranci.

To akan haka ne Sashen Hausa na Muryar Amurka yayi tattaki zuwa shedkwatar rundunar tsaro ta JTF dake aikin tsaro a yankin Neja-Delta. Wakilin Muryar Amurka Lamido Abubakar ya ji ta bakin shugaban rundunar ta JTF wato Manjo Janar PJ Atewe akan kalubalen da suke fuskanta.

PJ yace “muna kokarin kaddamar da matakan da gwamnati ta fito da su, domin fuskantar wannan kalubale. Kuma maganar da nake yi yanzu, mun kama masu laifi sama da dubu daya. Kuma ana cigaba da gudanar da bincike domin gurfanar da su gaban kotu. Sa’annan kuma, muna cigaba da gudanar da sintiri kan masu satar danyen mai a yankin na Neja Delta. Kuma yanzu haka tsaye muke wajen ganin bayan wadannan bata gari.”

Ya kara da cewa “salon da ya bi, wajen gani an samu zaman lafiya a yankin na Neja Delta da ‘yan bindigar kan haifar da barazana, ba wai salo ne na fito-na-fito ba, da ‘yan bindiga, amma ya hada da bin hanyoyi na diflomasiyya, tare kuma da taimakawa al-umomi don ganin cewar an kai ga fahimtar juna. Ko a watan Afrilun da ya gabata dai, sai da kamfanin mai na Shell ya rufe wasu tashoshin tura danyen mai dake kudancin Ejo, da Ikeromo a Jihar ta Bayelsa, sakamakon barazanar wasu ‘yan bindiga.

Bisa ga dukkan alamu dai, rundunar gamayyar tsaro ta JTF dake aikin tsaro a yankin Neja-Delta zata fuskanci sababbin kalubale na tsaro wanda kuma kyawun shugabanci zai yi tasiri matuka wajen shawo kan sa.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kama Mutane Dubu a Neja-Delta – 3’35”