Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Zai Yi Mulki da Adalci-inji Ateke Tom


Sabon shugaba Muhammad Buhari
Sabon shugaba Muhammad Buhari

Tun da shugaba Jonathan ya sha kaye a zaben 2015 ake tababan ko za'a samu zaman lafiya a yankin Niger Delta mai albarkatun man fetur.

Rarrabuwar kawunan 'yanbindigan Niger Delta ya kara tsorata mutane saboda babu wanda ya san abun da ka iya faruwa tunda dansu ya fadi zabe.

Tambaya ita ce shin kungiyoyin 'yanbindigan zasu ba sabuwar gwamnatin da Janar Buhari zai jagoranta goyon baya.

Daya daga cikin manyan shugabannin kungiyoyin 'yanbindigan Niger Delta Ateke Tom ya zanta da Muryar Amurka inda ya bayyana nashi ra'ayin da matsayin yaran da yake jagoranta.

Chief Ateke Tom ya bayyana cewa shi kansa da yaransa zasu ba Janar Buhari da sabuwar gwamnatinsa cikakken goyon baya. Yace ina kyautata zato Janar Buhari zai yi mulkin kasar da adalci. Yace na yi murna da nasarar da ya samu. Yace muna batun yankin Niger Delta. Yanzu za'a samu kwanciyar hankali a yankin fiye da da. Yace kodayake wasu yaran suna barazanar komawa sunkuru, "babu wanda zai koma sunkuru cikinsu". "Duk wanda ya koma sunkuru, to dan ta'ada ne"

Wadanda suka san Ateke Tom sun bayyana ra'ayoyinsu a kansa.Wata Hajiya Asabe tace ta san yana kaunar 'yan arewa.Tace lokacin da zabuka suka karato 'yan arewa na gudu suna komawa arewa. Shi ya tashi yace menene dalilin da suke komawa arewa. Yace kada su damu zai sa yaransa su kare 'yan arewa. Idan ma yaran sun soma rigima yana yi masu kashedi kada su taba 'yan arewa.

Ga cikakken rahoton Lamido Abubakar Sokoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG