Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: An Kaiwa Masu Jefa Kuri'a Hari A Jihar Rivers


Yadda aka rarraba kayan aikin zabe
Yadda aka rarraba kayan aikin zabe

A dai dai lokacin da zaben shugaban kasa da na 'yan majilisar dokokin tarayya ya gudana a sassa daban-daban na Najeriya.

Rahotanni daga jihar Ribas da ke yankin Niger Delta, na cewa wasu 'yan bindiga sun kai wa al’ummar Hausawa farmakiwata mazaba dake da suna Mazaba ta biyar a birnin Fatakwal dake jihar Ribas.

Wannan lamarin dai ya faru ne a lokacin da wasu yan asalin Arewacin Najeriya ke kokarin kada kuriaar su gad an takarar da suke so a mazabar.

Jamaa da dama dai sun jikkata kuma wakilin Muryar Amurka ya ziyarci daya daga cikin asibitin da aka kwantar dasu domin jin yadda lamarin ya faru kuma ga abinda wasun su ke cewa

‘’Sunana Abaca Mustafa na ce sai dai na jefa wa APC daga nan suka fara duka na, suka dole sai na saka nace ba zan saka an buge ni da sanda kuma aka fasa mani kwalba guda 4, da sandan ne dai suka faffasa mani jiki naji ciwo a kafa da hannaye biyu’’

Shima mutun na biyu ga abinda yake cewa

“Ni dai nazoo wajen zabe an bani kati inzo in dangwala sai naje na dangwala wa raayi na to ashe vakwai mai lura dani shine sai yaje ya gaya wa yaran cewa ga abinda yake faruwa suka fito dani daga cikin stadium suka fara duka na suka fasa mani kwalabe akai’’

“Sunana Mohammed Dahiru nazo kawai zanyi zabe basu mani kome ba sai da suka bari naanshi takardu sai suna cewa in dangwala ma PDP sai na dangwala wa APC kawai ina gamawa kawai sai suka jawo ni sai suka shiga dani kwana suka kama dukana, sai wani kuma ya dauko kwalba sai ya fasa mani aka sai gaskiya an nuna muna bamu da iznin muyi zabe an nuna muna mun fito daga wani waje kamar mu ba yan Najeria ba domin muna nan wajen zaben aka zo da bindigogi, shi dan takaran dan majilisa wasu ma'aikata ne suka yo masa rakiya suka zo nan suka hana mu zabe’’

Mohammed Kidaya Mohammed dai shine mai Magana da yawun rundunar yan sandar jihar Rivers kuma ga abinda yake cewa.

“Mun dai samu labarin wasu yara bata gari suna sace akwatin zabe kuma yanzu haka mun kame biyu daga cikin su kuma muna nan muna bincike’’

Sai dai da aka tambaye shi ko rundunar yan sandar jihar nada labarin an kai wa wasu yan arewacin Najeriya hari kuma waun sun a kwance asibiti yanzu haka anan sai amsa da cewa

‘’Ban zance naci maka musun hakan bai faru ba, kuma idan hakan ya faru to aba a sanar damu ba’’

Jihar Rivers dai na huskantar hare-haren siyasa, domin wasu sunyi musayar wuta a yankin Ogoni yankin da yake mahaifan dan takarar gwamna ne na jamiyyar APC wato Dr Dakuku Peterside, haka kuma ansamu dauki ba dadi a karamar hukumar akokotoro

XS
SM
MD
LG