An Kai Wa Saudiyya Hari Da Makami Mai Linzami

Saudiyya.

Sojojin kasar Saudiyya sun dakile wani harin makami mai linzami da 'yan tawayen Houthi na Yamal suka harbo.

Kafar yada labarai ta gwamnatin Saudiyya ta rawaito cewa kasar ta kakkabo wani makami mai linzami da aka harbor daga kasar Yamal, wanda aka harba zuwa filin jirgin sama na King Khalid dake arewa maso gabashin Riyadh.

‘Yan tawayen Houthi a Yamal, wadanda kasar Iran ke marawa baya, sune suka ‘dauki alhakin wannan hari, wanda sojojin Saudiyya suka dakile.

Jami’an Saudiyya sunce harin baiyi sanadiyyar asarar rai ba, ko wani babban ta’adi. ‘Yan tawayen Houthi sunce sun auna filin saukar jiragen saman birnin Riyadh ne.

Kasar Saudiyya na jagorantar shirin ganin an dakile mayakan Houthi a kasar Yamal, amma tashin hankalin ya fara yaduwa a kasashen dake iyaka da Yamal.

A watan Yuli, Saudiyya ta kakkabo wani makami mai linzami a kusa da birnin Makkah, wanda aka harbor daga Yamal, wata guda kafin a fara aikin hajji.