A kalla mutane biyar ne aka kashe, biyo bayan fashewar wani Bom a wata kasuwa dake garin Diffa a kudu maso gabashin Nijar Lahadinnan, biyo bayan dakile wani harin Boko Haram akan garin dake bakin iyaka.
WASHINGTON, D.C —
Wannan shine hari na biyu da Boko Haram ta kai a cikin kwanaki uku a yankin kudancin Nijar, inda wasu sojojin Chadi su 2,500 suka taru gabannin fara kai hare-hare akan kungiyar mai tayar da kayar baya.
Majalisar Tarayya a Nijar, Litinin dinnan zata jefa kuri’a akan wani kuduri da zai aika sojojin kasar Najeriya domin yaki da Boko Haram.
Mazauna garin Diffa sun bayyana cewa sun ji karar harbe-harbe tsakanin karfe 6 zuwa 10 na safe, a kudancin kasar.
“An yi fada tsakanin jami’an tsaro da ‘yan Boko Haram da suka yi kokarin shiga garin,” a cewar wani jami’in tsaro. “Anyi bata kashi a kusa da gadar Doutchi. Jama’a da yawa sun rasu.”