Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Tana Da Mayaka Dubu 4-6-inji Hukumomin Leken Asiri Na Amurka


Sojojin Chadi na samun galaba akan Boko Haram a bakin iyakar Najeriya, Fabrairu 5, 2015.
Sojojin Chadi na samun galaba akan Boko Haram a bakin iyakar Najeriya, Fabrairu 5, 2015.

Wadannan alkaluma suna zuwa ne yayinda kungiyar take zafafa kai hare hare a yankin.

Jami'an leken asiri na Amurka sun fada jiya jumma'a cewa, sun hakikance Kungiyar Boko Haram tana da mayaka da suka kama duga dubu 4-zuwa dubu shida, a dai dai lokacinda kungiyar ta kaddamar da hare hare a yankin.
Jami'an suka ce sun hakikance har yanzu kungiyar tana garkuwa da 'yan mata su fiyeda metan 'yan makaranta, wadanda ta sace cikin watan Afrilun bara, ta karkasasu zuwa sansanoni daban daban.
Ma'aikatan leken asirin suka ci gaba da cewa, duk da ikirarin da Boko Haram tayi a baya bayan nan cewa tayi mubaya'a ga kungiyar ISIS mai cibiya a Syria da Iraqi, Amurka bata jin kungiyar ta nemi, ko tana samun mayaka daga waje

Boko Haram tayi shekaru biyar tana tada kayar baya a cikin Najeriya, a wani yunkuri wai na neman kafa tsarin shari'a a yankin, hare haren da kungiyar take kaiwa yanzu sun karu sosai, kuma sun bazu zuwa kasashe makwabta da suka hada da kamaru da Nijar.

A jiya jumma'a, mayakan Boko Haram, suka kai hari kan garuruwa biyu a makwabciyar kasa, watau Nijar, amma sojojin cadi da Nijar din, suka koresu. Ministan tsaro na Nijar yace sojojin kasarsa sun kashe 'yan binidgar 109, lokacinda suka so su kai hari kan garuruwan Bosso da Diffa. NIjar kuma tayi hasarar sojoji hudu.
Ma'ikatar harkokin wajen Amurka da kakkausar lafazi tayi Allah wadai da wadannan hare hare.

XS
SM
MD
LG