Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Boko Haram Sun Ji Jiki a Garin Fotokol na Kamaru


Shugaban Kamaru Paul Biya ya sha alwashin fatattakar Boko Haram daga kasar.
Shugaban Kamaru Paul Biya ya sha alwashin fatattakar Boko Haram daga kasar.

Boko Haram sun kai hari garin Fotokol na kasar Kamaru, to amma sojojin Chadi sun fatattake su.

Bayanai na dada tabbatar da cewa mayakan Boko Haram sun kai hari garin Fotokol da ke kasar Kamaru, to amma sojojjin Chadi sun fatattake su a garin na Fotokol bayan da ‘yan Boko Haram su ka jima sun a tayar da kayar baya a yankin. Wakilin Muryar Amurka a Kamaru, Danda Mamadu ya gaya wa abokin aikinmu Aliyu Mustapha cewa, cewa wannan karan, ga dukkan alamu, ‘yan Boko Haram ba su ji da dadi ba a wannan fafatawar da aka yi sa’o’i ana yi.

Ya ce Fotokol wani gari ne da ke cikin kasar Kamaru, cikin jihar arewa mai nisa daura da kasar Chadi wanda ke fama da tashin hankalin Boko Haram, musamman saboda ya na kan iyaka kuma babu wani tsattsauran matakin tsaro a garin, kuma gashi garin na kusa da Gamborun Ngala da ke Nijeriya. Ya ce tunda sojojin Chadi su ka zo kasar Kamaru da nufin yakar Boko Haram su ka yi ta fatattakarsu, su ka kashe na kashewa. Ya ce a baya-bayan nan sun shafe sa’o’i biyar sun a ta musayar wuta. Ya ce sojojin Chadi sun gano cewa ‘yan Boko Haram sun maida yankin . Y ace lallai an kashe ‘yan Boko Haram da dama a fafatawar baya-bayan nan, kodayake su ma sojojin Chadin an kashe wasunsu kalilan. Ya ce saboda nuna goyon bayansu, matan sojojin Chadi sun dafa abinci su ka kai ma sojojin da ke jinya a birnin Njamena.

Da aka tambaye shi gaskiyar labarin da ke cewa ‘yan Boko Haram ba ‘yan kasa guda ba ne sai y ace lallai da alamar haka; akwai ‘yan Nijeriya, da ‘yan Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya, akwai ‘yan Chadi da ‘yan Nijar. Y ace baya ga tababan da ake da ita kan ko shin ‘yan Boko Haram ‘yan wa’enne kasashe ne, akwai kuma tambayar da ake kan ko shin wasu na rabewa da Boko Haram suna tafka wasu nau’ukan ta’asa.

Mayakan Boko Haram Sun Ji Jiki a Garin Fotokol na Kamaru - 4'30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:30 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG