An Kafa Dokar Ta Baci A Wasu Gundumomin Yankin Tilabery

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bada sanarwar kafa dokar ta baci a wasu gundumomin yankin Tilabery, da nufin baiwa jami’an tsaro cikakken hurumi a yakin da kasar ke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda da na ‘yan fashin da suka addabi jama’a.

Taron majalisar ministocin da ya gudana a jiya juma’a ne ya bada sanarwar kafa dokar ta baci, a gundumomin Tera Say da Torodi, bayan la’akari da yawaitar kashe kashe da sace sacen dukiyoyin jama’a, sakamakon matsalar tsaron dake da nasaba da halin da ake ciki a kasashe makwafta wato Mali da Burkina Faso.

Kakakin gwamnatin Nijar minista Abdourahamna, a wata tattaunawar wayar tarho yace, sa’o'i kalilan bayan daukar wannan mataki wasu ‘yan bindiga sun hallaka wani jami’in Douanes kokuma kwastom a wata tashar binciken Tera, to amma tuni jami’an tsaro su ka yi nasarar kama daya daga cikin wadannan mahara inji gwamnatin Nijar.

Yankin Tilabery na daga cikin yankuna uku dake cikin karkashin dokar ta baci, tun a shekarar 2017, bayan lura da yadda ‘yan ta’addan Mali ke shigowa domin kai hare hare kamar yadda rikicin boko haram a Arewa maso gabashin Najeriya ya yi, sanadiyar daukar irin wannan mataki a yankin Diffa ko da yake talakawa na korafi a game da yadda matakin ya haifar da tsayawar harokokin yau da kullun a yankin.

Your browser doesn’t support HTML5

Jamhuriyar Nijar: An Kafa Dokar Ta Baci A Wasu Gundimomin Yankin Tilabery