Babban hadimin shugaban kasar Mallam Garba Shehu ya fadawa manema labarai cewa ziyara da shugaban zai kai a ranar Laraba zuwa Maiduguri zata baiwa shugaban damar gane mataki nag aba da zai dauka bayan bayanai da zai samu daga jami’an tsaron da kuma abubuwa da zai gani a wurin.
Mallam Garba Shehu ba zai iya bada takamaiman abin da shugaban kasa zai fada a wurin ziyarar ba, amma yana ganin wannan ziyarar zata taimakawa wurin daukar matakanda suka dace wurin daikle harkokin mayakan Boko Haram kuma yace zai shugaban ya isa Maiduguri za a samu cikakken bayani.
Mallam Garba Shehu ya tabbatarwa manema labarai cewa shugaba Buhari na sane da irin hare haren kwantan bauna da ‘yan ta’adda ke kaiwa sojojin Najeriya kuma yace hakan ne yasa shugaban ke gudanar da tarurruka da ministocinsa da shugabannin hukumomin tsaron kasa a cikin wannan lokaci domin duban irin bukatu rundunar Najeriyar a yaki da ‘yan ta’adda.
A cikin wannan lokaci dai, mutanen yankin arewa maso gabashin suna kira ga shugaba Buhari ya yi garanbawul a shugabancin tsaron kasar, abin da suka ce zai taimaka ainun wurin kawo karshen wannan da Boko Haram
Ga hirar wakilinmu a Abuja Umar Farouk Musa da mallam Garba Shehu:
Facebook Forum