Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Rufe Ofishin Jakadancinta A Congo Bisa Barazanar Ta'addanci


Shugaban kasar Congo Joseph Kabila
Shugaban kasar Congo Joseph Kabila

Amurka ta rufe ofishin jakadancinta na kasar jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo saboda wasu bayanai da ta samu na gaskiya dake nuni da barazanar ta’addanci.

Ofishin jakadancin dake birnin Kinshasa zai ci gaba da zama a rufe har zuwa yau Talata, an kuma shawarci duk Amurkawan dake kasar jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, kar su bayyana kansu.

Sai dai gwamntin Congo na zargin Amurka da shirya wannan labari na tsoratarwa ta hanyar rufe ofishin jakadancinta.

Haka kuma ta ce Amurka da sauran mutanen da basu da iko kan harkokin zaben kasar, suna kokarin dauke hankalin masu kada kuri’a ne gabannin zaben shugaban kasar dake tafe ranar 23 ga watan Disamba.

Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta kwashe shekaru biyu ta na kokarin gudanar da zabe don maye gurbin dadadden shugaban kasa Joseph Kabila.

Kamata ya yi shugaba Kabila ya sauka daga kan mulki a shekarar 2016 lokacin wa’adinsa na karshe ya kare. Amma ya yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima ta yadda ya bashi damar ci gaba da mulki har sai an zabi sabon shugaban kasa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG