Da maraicin jiye ne wasu ‘yan bindiga suka yi kai hari a kan birnin na Maiduguri ta hanyar ta da bama bamai a jikin wasu mata ‘yan kunar bakin wake.
Ya zuwa yanzu babu wani rahoto da ya tantance adadin yawan mutanen da suka jikkata a wannan hari.
Tun da misalin karfe shida na maraici mazauna garin na Maiduguri da kewaye suka fara jin harbe-harbe da tashin bama bamai a wani yunkuri da maharan suka yi na kutsa kai cikin birnin.
Sai dai rahotanni sun ce rundunar sojin yankin ta dakile wannan yunkuri inda ta fatattakin maharan, lamarin da ya sa aka kafa dokar hana fita ta tsawon sa’oi 24.
Amma wasu rahotanni sun ce a jiya Laraba wasu daga cikin matan da maharan suka yiwa damara da bamai bamai sun samu kutsawa cikin mutane inda suka tarwatsa bama baman akan wasu mata.
Sai dai har yanzu babu wani karin bayani da hukumomi suka game da wannan hari amma wasu mazauna birnin sun gayawa wakilin Muryar Amurka cewa harin ya rutsa da mutane da dama.
Wannan hari na zuwa ne kwanaki kadan bayan wani da aka kai a garin Gulde da ke karamar hukumar Askira Uba a kudancin jahar ta Borno da ke arewacin Najeriya inda suka halaka mutane da dama.
Ga karin bayani daga wakilin Haruna Dauda dake birnin Maiduguri:
Your browser doesn’t support HTML5