Kasar Najeriya ta kara yunkurawa domin ganin ‘yan kasar sun tafi daidai da zamani da kuma rage dogaro kacokam ga amfani da motoci masu amfani da man fetur ko iskar gas.
Ba da jimawa ba ne ‘yan Najeriya suka shedi mota ta farko da aka hada a kasar mai aiki da wutar lantarki maimakon shan man fetur ko gas.
Sai dai bisa la'akari da yadda wutar lantarki take a Najeriya, masana ke ganin cewa dole a samar da wata hanya ta cajin wadannan motocin mafi karfi da inganci a cewar tsohon Daraktan Hukumar Makamashi ta kasa Farfesa Abubakar Sani Sambo.
Hukumar kula da zayyana motoci ta Najeriya ta dukufa ga aikin samar da tashoshin cajin wadannan motocin masu inganci guda uku a kasar inda aka kammala wadda aka yi a jami'ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato.
Masana kare muhalli sun ce shi kansa muhalli yanzu zai samu kyautatuwa sanadiyyar fara amfani da irin wadannan motocin a cewar masanin muhalli Mu'azu Ahmadu Suka.
Wannan tashar da sauran biyu da ake sa ran a kammala a Jami'o'in Lagos da Nsuka ana sa ran su kasance cibiyoyin kula da motocin da kuma bincike kan kara inganta cajin ta amfani da hasken Rana.
Saurari Rahoto Ciki Sauti Daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5