An Kaddamar Da Shimfida Bututun Mai Tsakanin Nijar Da Benin

A jamhuriyar Nijar shugaba Issouhou Mahamadou ya jagoranci bukin kaddamar da aiyukan shimfida bututun mai, wanda idan aka kammala zai bada damar isar da man kasar daga rijiyoyin Agadem yankin Diffa zuwa jamhuriyar Benin.

A kauyen Koulele na yankin Diffa ne shugaba Issouhou Mahamadou ya jagoranci bukin kaddamar da aiyukan shimfida wannan bututu da zai hada rijiyoyin man Agadem da tashar jirgin ruwan Seme dake jamhuriyar Benin.

A kalla milliard ko biliyan 2400 na kudin cfa ne ake saran kashewa kafin a kammala wannan aiki, abin da zai bada damar bunkasa tattalin arzikin Nijar inji ministan man fetur Foumakoye Gado.

Tuni dai ‘yan Nijar suka fara nuna farin ciki akan wannan yunkuri na hadin gwiwar China da Nijar.

A watan Nuwamba 2021 ne ake saran kammala wannan aiki da zai samar da aikin yi ga mutane a kalla 5000, sai dai Sidik Ali na kungiyar MITRAD na cewa akwai bukatar a yi takatsantsan.

Za dai a soma aiyukan shimfida wannan bututu mai tsawon kilomita 1982 a wani lokacin da rahotanni ke cewa danyen mai ya malala a kasa, sakamakon fashewar bututun dake hada rijiyoyin Agadem da matatar SORAZ a makon jiya.

A shekarar 2009 ne gwamnatin jamhuriyar ta biyar karkashin shugabancin Tanja Mamadou ta cimma yarjejeniya, da kamfanin CNPC na kasar China wacce a karkashinta aka fara hako man fetur a rijiyoyin man Agadem tare da gina matatar SORAZ a Zinder, kafin daga bisani a fara sayar da shi a kasuwannin kasar a shekarar 2012.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Za'a Shimfida Bututun Mai Tsakanin Kasashen Jamhuriyar Nijar Da Benin