An Jaddada Hukuncin Daurin Rai Da Rai Akan Mladic, Mai Kisan Gillar Bosnia

Ratko Mladic yayin da ake shirin yanke masa hukunci

Shugaba Biden ya ce “wannan hukunci mai dumbin tarihi, na nuni da cewa duk wadanda suka aikata wasu munanan ayyuka, za su fuskanci kuliya. Sannan hukuncin na kara nuni da yadda muka himmatu wajen ganin an kaucewa sake aukuwar irin wannan danyen aiki a ko ina a duniya.

Sashen da ke hukunta manyan laifuka na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da hukuncin daurin rai da rai ga tsohon Kwamandan rundunar Sabiyawan Bosniya Ratko Mladic, wanda ake masa lakanin da "Butcher of Bosnia." An same Mladic da laifukan kisan kare dangi, laifukan cin zarafin bil'adama, da kuma laifukan yaki da aka aikata a lokacin yakin Bosniya daga 1992-1995.

Shugaba Joe Biden ya yi marhaban da wannan hukunci a cikin wata sanarwa inda ya ce, "tunanina a yau yana tare da dukkan iyalai da suka tsira daga ukubar Mladic. Ba za mu taba iya mantawa da mutuwarsu ba, amma ina fata hukuncin yau zai ba da kwanciyar hankali ga duk waɗanda ke cikin baƙin ciki. "

A matsayinsa na tsohon Kwamandan Sojojin Sabiyawan Bosniya, Mladic babban jigo ne a danyen aikin da aka aikata na na share al’umar Bosniak da Croats da ke Bosnia and Herzgovina daga yankin da ke karkashin Sabiyawa, ciki har da kisan sama da Musulmi 8,000 manyan da yara a garin Srebrenica a shekarar 1995.

“Laifukan da aka aikata a Bosnia da Herzegovina, na daya daga cikin munanan lokuta bayan da wanda aka gani a lokacin yakin duniya na biyu, a cewar Sakataren harkokin wajen Amurka Blinken kamar yadda ya fada a wata sanarwa.

Sakatare Blinken ya ce "Duk da kokarin da masu yin hakan suke yi na rufe bakin shaidu, da kaucewa sammacin kamawa, adalci ya tabbata a wannan lamarin. "Muna yaba wa jajircewa da juriyar wadanda suka tsira da kuma danginsu wadanda suka ci gaba da gwagwarmaya don a amince da cewa an aikata wadannan laifuka a hukumance."

Yayin da bikin cika shekaru 26 na kisan kare dangi a Srebrenica ke gabatowa, Sakatare Blinken yana mai fatan cewa "hukuncin da Kotun daukaka kara ta yanke ya ba da kwanciyar hankali ga wadanda abin ya shafa da danginsu." Ya kuma bayyana godiyarsa ga shekarun da kotun ta kwashe na ganin an tabbatar da adalci a shari'ar Mladic.

Shugaba Biden ya ce “wannan hukunci mai dumbin tarihi, na nuni da cewa duk wadanda suka aikata wasu munanan ayyuka, za su fuskanci kuliya. Sannan hukuncin na kara nuni da yadda muka himmatu wajen ganin an kaucewa sake aukuwar irin wannan danyen aiki a ko ina a duniya.