Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Na Tsananin Hukunta Masu Yin Addini


Hotunan shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un da mukarrabansa gwamnatinsa da aka samo daga KCNA
Hotunan shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un da mukarrabansa gwamnatinsa da aka samo daga KCNA

Amurka na ci gaba da “nuna damuwa matuka game da cin zarafin bil adama da [Korea ta Arewa] ke yi, ciki har da tsananin takunkumin da ya shafi 'yancin yin addini,” in ji Babban Jami’in Ma’aikatar Harkokin Waje, Daniel Nadel.

A cewar Rahoton 'yancin Addini Na Duniya na baya-bayan nan, gwamnatin Koriya ta Arewa, na ci gaba da aiwatar da kisa, azabtarwa, kame, da cin zarafin mutanen da ke harkar kusan kowane addini. Rashin samun dama da kuma rashin cikakken bayani a kan lokaci, na ci gaba da kawo cikas ga wadatar bayanan da suka shafi shari'o'in cin zarafi na kowani mutum.

Kungiyar nan mai zaman kanta mai suna Open Doors USA. ta kiyasta cewa a ƙarshen shekara, ’yan Koriya ta Arewa dubu 50 zuwa 70,000 suna cikin kurkuku saboda kasancewarsu Kiristoci. A watan Mayu na shekarar 2020, kungiyar sa kai ta Christian Solidarity a duk duniya ta kiyasta cewa ana tsare da mutum 200,000 a sansanonin ‘yan fursuna, galibinsu saboda mabiyan addinin Kirista ne.

Cibiyar Bayar da Bayanai don 'Yancin Dan Adam na Koriya ta Arewa, wacce kungiya ce mai zaman kanta ta Koriya ta Kudu, ta ambaci wadanda suka sauya sheka da suka isa Koriya ta Kudu daga 2007 zuwa Disambar 2019 da wasu kafofin, sun ruwaito cewa an take hakkin kimanin mutum 1,411 sun yi addini don sun yi addini har da abinda ya hada da kisa akalla mutum 126 da kuma wasu 94 da suka bata.

A watan Oktoba na 2020, wata kungiyar mai zaman kanta da ke da tushe a Burtaniyya mai suna Korea Future Initiative, ko kuma KFI, ta fitar da rahoto dangane da hirarraki da ta yi da mutum 117 wadanda suka yi ridda kuma suka tsira, da shaidu, ko kuma masu cin zarafin 'yancin addini daga 1990 zuwa 2019.

Masu binciken sun gano waɗanda aka azabtar da su 273 saboda aikata laifin a aikin addini ko yin hulɗa da masu addini, ko halartar wuraren ibada, ko kuma aikin da ya shafi bauta.

Rahoton na KFI ya ce an kama su, an tsare su, an yi musu tambayoyi na tsawon lokaci, ko hukunta danginsu, azabtarwa ko ci gaba da cin zarafinsu ta hanyar lalata, ko tilasta musu zubar da ciki, ko kisa, da hukunci a bainar jama'a.

A shekarar 2020, a karo na 19 a jere, Open Doors Amurka ta sanya Koriya ta Arewa a matsayi na daya a rahotonta na shekara na rahoton Duniya na kasashen da kiristoci suka dandana “tsananin hukunci”. Kungiyoyi masu zaman kansu da wadanda suka sauya sheka sun ce gwamnati galibi tana amfani da wata manufa ta kame ko kuma hukunta dangin Kiristocin.

A cewar Open Doors USA, "Idan aka gano Kiristocin Koriya ta Arewa, akan tisa keyarsu zuwa sansanonin kwadago a matsayin masu laifi na siyasa ko ma a kashe su nan take."

Amurka na da niyyar sanya batutuwan da suka shafi hakkin bil adama a matsayin manyan manufofinta na kasashen waje, in ji wani Babban Jami'i Nadel. Wannan ya hada da "hukunci ga wadanda suka aikata wadannan cin zarafin" kan 'yancin addini a Koriya ta Arewa.

XS
SM
MD
LG