An iya Ceto Mutane 15 Daga Hadarin Jirgin Sama a Taiwan

Ma’aikatan ceton rai sun yi amfani da motar daga kaya wajen dago garwar jirgin pasinjan da ya fadi a wajen garin Taipei, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 20, wasu da yawa kuma ba amo ba labarinsu.

Ma’aikatan ceton rai sun yi amfani da motar daga kaya wajen dago garwar jirgin pasinjan da ya fadi a wajen garin Taipei, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 20, wasu da yawa kuma ba amo ba labarinsu.

Jirgin na TransAsia Airways ya tunkuyi wata gada ne, bayan haka ya fada cikin rafin Keelung, jim kadan bayan tashinsa yau laraba.

Sau ran kiris jirgin dai ya kara da wasu gine-ginen benaye da yawa dake wurin.

Tuni dai Masu aikin ceton rai suka kewaye inda jirgin ya fadi cikin kwale-kwale, kuma sun iya cetar akalla mutane 15 ciki har da wani karamin yaro.

Your browser doesn’t support HTML5

A n iya ceto mutane 15 daga hadarin jirgin sama a Taiwan - 1'00"