Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muguwar Dusar Kankara Ta Mamaye Arewa Maso Gabashin Amurka


Dusar kankara ta rufe gidaje da motoci
Dusar kankara ta rufe gidaje da motoci

Dusar kankarar da ta mamaye arewa maso gabashin Amurka ba'a taba samun irinta ba cikin shekaru 143 da suka gabata.

Yau Litinin dusar kankara mai tsananin gaske wacce ake jin zata gurgunta harkoki a galibin arewa maso gabashin Amurka cikin kwanaki biyu masu zuwa, ta fara fatattakar yankunan da suka kama daga nan birnin Washington DC zuwa Boston.

Birnin Washington ya tsallake rijiya da baya, amma can arewaci a jihohin New Jersey da New York da Connecticut da Rhode Isalnd da Massachussetts sun ayyana dokar ta baci dangane da kankarar. Hukumomi sun bukaci daruruwan miliyoyin jama'a su zauna gida, a yayinda kamfanin jiragen kasa mai daukar fasinja da ake kira Amtrak ya rage zirga zirgar jiragensa, hakama an soke daruruwan jiragen sama na fasinja saboda tsammanin kara tsananin yananin a cikin daren nan na Litinin ko kuma safiyar Talatar nan, al'amari da zai dore har zuwa asubahin Laraba.

Ana sa yankin zai fuskanci dusar na tsawon kafa uku, tareda iska mai karfin gaske, da kuma yiyuwar a sami ambaliya.

Mutane sun saye kayan abinci a galibin kantuna, da shebura da janaretoci, saboda shirin yin zaman gida na kwanaki.

Magajin garin New York Bill de Blaiso yace zata yiwu dusarkankarar ta kasance mafi muni da yankin ya taba fuskanta, har zai dara wacce yankin ya fuskanta shekaru 143 da suka wuce.

Jami'ai a yankin sun gargadi jama'a zasu fuskanci rashin wutan lantarki, watakil na kwanaki.

Gwamnan jhar New York Andrew Coumo ya bada umarnin hana tafiye tafiye baki daya daga daren yau Litinin, mataki da zai shafi kananan hukumomi fiyeda 12 a yankin.

XS
SM
MD
LG