Shugaban Houthi ‘yan Shi’a dake tawaye a Yemen ya kira a yi canjin gwamnati cikin lumana sa’o’i kadan bayansun sako wani ma’aikacin fadar shugaban kasar da suka tsare har na tsawon kwanaki goma.
Yayin da ya bayyana a kafar telibijan din ‘yan tawayen Abdel-Malek al-Houthi ya gayyaci duk wadanda ya kira masu ‘yanci da adalci’ zuwa wani babban taro da zai hada kowa da kowa a tarihin kasar, ranar Juama’a a Birnin Sana’a
Al-Houthi yace ya dauki matsayi akan masu son kawo rudu da kuma masu son a cigaba da fada da yin gaddama maimakon neman hadin kai.
Tun farko ‘yan tawayen suka sako ma’aikacin fadar shugaban kasar Ahmed Awad bin Mubarak kafin al-Houthi ya gabatar da jawabinsa a telibijan.
‘Yan tawayen sun cafke Mubarak ne daga motarsa lamarin da ya kaiga fafatawa tsakaninsu da masu gadin fadar shugaban kasar. Daga karshe dai alatilas shugaba Abd Rabbuth Mansour Hadi ya bar fadar ya kuma yi murabus.
Yanzu dai su ‘yan tawayen Houthin suka fi duk kungiyoyin dake fafitikar neman iko karfi a kasar tun shekarar 2012 yayin da aka yi wani hargitsin da ya hambarar da gwamnatin Ali Abdullah Saleh wanda ya dade yana mulki.