Attoni Janar kuma ministan shari'a na Amurka Eric Holder yace jami'an tarayya sun wargaza wani gungun 'yan leken asiri na Rasha a New York, inda mutane uku da ake zargi suka yi kokarin samun hadin kai daga wasu mazauna kasar domin suyi musu leken asiri.
Hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka FBI jiya Litinin ta kama Evgeny Ruryakov a unguwar Bronx.
Wasu mutanen biyu basa Amurka kuma suna da kariya ta difilomasiyya duk da haka an gabatar da tuhuma a kansu.
Kamar yadda takardun karar da ma'aikatar shari'a ta shigar, sun nuna cewa Burkayov ya karya dokokin Amurka saboda bai gayawa hukumomi cewa ya shigo Amurka a matsayin dan leken asiri ba. Yana aiki ne a ofishin wani bankin Rasha dake New York. Sauran mutanen biyu daya yan aiki ne a ofishin kasar dake Majalisar Dinkin Duniya, dayan kuma shine wakilcin harkokin cinikayyar kasar a ofishin jakadancinta.
Ana zargin su duka uku da kokarin tara bayanai kan takunkumin da Amurka ta aza kan bankunan Rasha, haka kuma su samo wasu hanyoyin habaka makamshi, baki daya su aike dasu wadannan bayanan ga hukumomin leken asirin Rasha.
Haka kuma ana zargin mutanen uku da yunkurin samun hadin kan mutane da tuni suka zama Amurkawa, wadanda suka hada da ma'aikatan wasu manyan kamfanoni da kuma mata a wasu manyan jami'o'in Amurka.
Samada shekaru 20 bayan kawo karshen zaman doya da manja, har yanzu masu aikin leken asiri daga Rasha suna cigaba da aiki a kasar, mataki da jami'an shari'a suka ce yana barazana gaharkokin tsaron Amurka.
Mutanen uku da ake tuhuma zasu fuskanci daurin shekaru 15 a gidan kaso idan aka samesu da laifi.