An Horas Da Matasa Fiye Da 15000 a Kokarin Rage Fatara

Matasa

A jihar Adamawa fiye da mutane 15000 hukumar samar da aikin yi ta kasa ta horas dasu a fannoni daban daban
A bikin raba kayan tallafi ma wadanda suka samu horo a fannoni daban daban jami'in samarda aikin yi ko NDE, a takaice, ya ce kawo yanzu mutane fiye da dubu goma sha biyar hukumar ta koya masu sana'o'i.

Alhaji Abubakar Aliyu jami'in NDE a jihar Adamawa ya ce babban dalilin horas da mutane musamman matasa da kuma taimaka masu da kayan aiki da taimakon kudi shi ne rage zaman banza da talauci a kuma inganta rayuwar jama'a. Ya ce rashin aikin yi tsakanin matasa yana daya daga cikin dalilan da suke jawo masifa ta tashin hankali a kasa. Ya ce fatara da rashin aiki su ne suka fi damun mutane. Idan mutane suna cikin damuwa to kuwa za'a samu tashin hankali. Irin horaswar da suka yi da tallafi suna taimakawa wurin kawo zaman lafiya.Ya kira mutane su bada hadin kai a hada karfi da karfe a horas da mutane domin inganta rayuwar al'umma. Ya ce hukumarsa ta bada karfi wurin koyawa mutane sana'a. Bayan hakan ana kuma taimaka masu su samu abun yi domin su ma su taimaki wasu.

Yayin da yake nashi jawabin a wurin bikin Sanato Ahmed Barata mai wakiltar kudancin Adamawa ya ce muddin ana son zaman lafiya to dole ne a samar ma mutane aikin yi musamman matasa.Nan gaba za'a zurfafa ilimin da za'a ba mutane domin su samu su kara cigaba, in ji Sanato Ahmed Barata.

Har yanzu a wurin bukin tsohon shugaban karamar hukumar Mayo Belwa ta kudancin jihar ya ce har yanzu suna neman ruwa da wuta da karfafawa ta wajen samun abun yi ma mutanen yankin. Suna bukatar hanyoyi da ma karin makarantu da gyara tsoffin da suke da su.

Wadanda suka samu tallafi sun bayyana farin cikinsu. Wasu ma sun yi mamaki sun samu abun aiki. Sun yi godiya ga gwamnati da ta shirya masu irin horon da suka samu lamarin da zai kyautata rayuwarsu da na 'yanuwansu da ma jihar.

Ibrahin Abdulaziz nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Horas Da Matasa Fiye Da 15000 A Kokarin Rage Fatara - 3:04