Shugaban makarantar Dr. Umar Gurama Dukku wanda a karkashinsa matasan suka samu horaswar ya ce kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.Ya ce abun da ya faranta masa rai shi ne wasu mata da suka koyar da su, lokacin sallar layya maimakon su sayi lemun kwalba da aka saba saya can baya sai suka yi lemun sha na tumatur domin baki. Duk wanda ya sha sai ya tambaya ina suka samo irin wannan lemun. To sai su amsa su ce yana cikin abun da aka koya masu a Dadinkowa. Ya ce akwai wata ma a jihar Zamfara wanna lemun ta keyi idan za'a yi buki a kuma biyata, wato ita ta samu sana'a.
Ban da yin lemun tumatur an koyawa matasan yadda zasu shuka su mangwaro da gwaiba da lemu. Sun soma samun rahotanni cewa wasu 'yan siyasansu sun taimaka masu sun soma shuka domin su tsayar da tasu sana'ar. Sakamakon da makarantar ke samu ya nuna koyaswar da suka yi ma matasan ya soma haifar da da mai ido.
Matasan da suka ci gajiyar shirin su ma sun fadi albarkacin bakinsu. Wani ya ce ya dasa gwanda yadda aka koya masu. Ya kuma yafa barkono da wasu tsiron. Ya ce duk sun fito da kyau kuma bai yi asarar ko daya ba. Wadanda suka yi magana sun ce sun karu da abubuwan da aka koya masu sun kuma kira gwamnati ta kara yi masu taimako.
Sa'adatu Fawu nada karin bayani.