Sarakunan sun yi kiran ne yayin da suka kammala taronsu a garin Lesha Barba. Sarkin Fulani Alhaji Shehu Sale ya ce abun da ya fi damunsu shi ne rashin burtali domin duk an nomesu da kuma rashin ruwa. Alhaji Sale ya ce sun sha fada ma gwamnati da jami'an kananan hukumomi su kula da matsalar dake damun Fulani a jihar ta Kwara. Duk da rashin kulawar gwamnati amma suna karban jangali a wurin makiyayan.
Da can Sanato Shaba ya yi alkawarin za'a gyara masu kara har ma an auna amma shiru kamar an shuka dusa. Akwai kuma matsalar makaranta. Suna dasu a wasu wurare. Kamar Lesha Barba makaranta daya ce suke da ita wadda yau shekararta shida. To amma aji daya kawai gwamnati ta gina. Makiyayan sun kara daya amma wasu yaran a waje suke daukan karatu. Dangane da malamai makiyaya ne ke biyan albashin malamai uku, kana idan yaransu sun kammala karatun firamare basu da sakandaren da zasu iya zuwa. Wadannan abubuwa suke rokon gwamnatin Kwara ta yi masu.
Hassan Umar Tambuwal nada rahoto.