An Gurfanar Da Wasu Ma'aurata Da Laifin Kisan Kai Game Da Mutuwar 'Yarsu Mai Matsananciyar Kiba

Kaylea Titford

An tuhumi wasu iyaye biyu da laifin kisan kai bayan da aka zarge su da barin diyarsu ta yi mummunar kiba a cewar jaridar The Telegraph.

A wani lamari da ake kyautata zaton shi ne irinsa na farko, iyayen Kaylea Titford, mai shekaru 16, sun gurfana a gaban kotu a ranar Talata, bayan da aka tuhume su da laifin yin sakaci da ya yi sandiyar mutuwar ‘yar su.

An tsinci yarinyar da ke da nakasa a gidansu da ke Newtown, Powys, a Wales, a watan Oktoban 2020.

An yi zargin cewa tsakanin Maris 24 da Oktoba 11, 2020, mahaifin Kaylea Alun Titford, 44, da mahaifiyarta Sarah Lloyd-Jones, 39, sun kasa tabbatar da cewa an biya mata bukatunta na cin abincin mai inganci, lamarin da ya haifar da mummunar kiba.

Haka kuma ba su tabbatar da cewa ta samu isasshen motsa jiki ba, da zaune cikin yanayin tsafta ba, da samun tsabtattaccen muhalli, da kula da lafiyar jikinta nemam taimakon jinya, in ji tuhumar.

Ma'auratan sun bayyana a gaban Kotun Majistare ta Welshpool a ranar Talata kuma sun tsaya tare a sanye da takunkumin rufe hanci. Sun yi magana ne kawai don tabbatar da sunayensu, shekaru da adireshinsu, amma ba su shigar da koke ba.

Za su bayyana a gaban Kotun Mold Crown ranar 14 ga Afrilu.

An yi imanin wannan ne karon farko da ake tuhumar iyaye da irin wannan laifin.

- Wannan labarin na jaridar Telegraph ne wanda Hadiza Kyari ta fassara